Me ka ke nema?


Shafin Farko

Barka da Zuwa Masarautar Bichi



Mai Martaba Sarkin Bichi
Alhaji Nasir Ado Bayero A Fada
Hoto:  Twitter: hrh_nasir_ado_bayero


Gabatarwa

Bichi, gari ne mai daɗaɗɗen tarihi. Shi ne matsugunnin ƙaramar hukumar Bichi, fadar Gundumar Bichi sannan kuma fadar Masarautar Bichi, da ke cikin Jahar Kano da ke Najeriya.

Sabuwar masarauta ce da Mai Girma Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, OFR, Khadimul Islam ya kafa ta a shekarar 2020 biyo wa bayan buƙatar da ke akwai na faɗaɗa masarutun jahar Kano domin kusantar da jama’a da gwamnati da kuma kusanta gwamnati da jama’a.

Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne ya zama sarki na farko a wannan masarauta, sannan kuma bayan ɗaukaka likafarsa zuwa kan kujerar da mahaifinsa ya bari, Alhaji (Dr) Ado bayero; wato naɗin da aka yi masa a matsayin sabon sarkin Kano na goma sha biyar a cikin jerin sarakunan Fulani a Kano, sai ƙaninsa Alhaji Nasir Bayero ya maye gurbinsa.

Sarakuna


Kasuwanni


Bukukuwa


Wasu Gurare


Yaƙuƙuwa


Ƙofofin Bichi


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub